Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’in Kasar nan (JAMB) ta tsayar da ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar rubuta jarabawar gwaji wato Mock Examinations.
Hukumar ta shirya wannan jarabawa na gwaji ne domin dalibai su koyi amfani da na’uran komfuta da kuma yadda tambayoyin jarabawar za su kasance.
Jami’in hukumar Fabiyan Benjamin ya sanar da haka a ranar Talata inda ya kara da cewa dalibai za su iya fara buga takardar da zai baka daman shiga dakin rubuta jarabawar daga ranar 6 ga watan Maris.
Benjamin yace har yanzu dai hukumar ba ta tsayar da ranar rubuta ainihin jarabawar ba amma wata majiyar ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa za a rubuta jarabawar ranar 16 ga watan Afrilu.
Idan ba a manta ba hukumar JAMB ta fara siyar da fom din JAMB tun a ranar 10 ga watan Janairu sannan ta rufe siyar da fom din ranar 21 ga watan Fabrairu.
A lokacin ta tsayar da ranar rubuta ainihin jarabawar ranar 16 zuwa 23 ga watan Maris amma dage zabe da aka yi ya sa hukumar ta dakatar da rubuta jarabawar.
Sai dai har yanzu hukumar bata sanar da ranar da za a fara rubuta ainihin jarabawar ba.
Discussion about this post