‘Yan takarar gwamna 10 za su mara wa PDP baya a zaben jihar Adamawa

0

‘Yan takarar kujerar gwamna na jam’iyyu 10 a jihar Adamawa sun amince su mara wa jam’iyyar PDP baya domin ganin dan takaran jam’iyyar da ke neman kujerar ya samu nasara a zaben da za a yi ranar Asabar 9 ga watan Maris.

Wadannan ‘yan takaran sun hada da Sadiq Khaliel na jam’iyyar MRDD, Danjuma Musa na jam’iyyar FJP, Naziru Sa’ad na jam’iyyar ZLP, Ahmed Hassan na jam’iyyar DA, Salihu Danjuma na jam’iyyar APM, Abdullahi Usman na jam’iyyar NCP, Bappari Umar na jam’iyyar KOWA, Lami Musa na jam’iyyar PPN, Elizabeth Isa na jam’iyyar CAP da Frank Simon na MEGA party.

‘Yan takaran sun yanke wannan hukuncin ne bayan wata zama da suka yi da dan takaran kujerar na jam’iyyar PDP Umaru Fintiri a Yola ranar Litini.

Elizabeth Isa daga jam’iyyar CAP ta bayyana cewa ta amince ta mara wa Fintiri baya a zaben ne saboda kyawawan halayen da yake da shi sannan don ci gaban jihar.

Shi kuwa Bappari Umar na jam’iyyar KOWA yace zai mara wa Fintiri baya ne a zaben gwamna amma ‘yan takaran kujerun majalisar dokoki daga jam’iyyar su za su fito domin a fafata zabe da su.

A karshe Fintiri ya godewa wadannan ‘yan takara sannan bisa wannan goyon baya da suka nuna masa.

Share.

game da Author