Ana gab da kammala gina dakunan adana magunguna a kasar nan

0

Shugaban hukumar ICRC Chidi Izuwah ya bayyana cewa ana gab da kammala gina dakunan adana magunguna a kasar nan.

Izuwah ya ce USAID, Asusun Duniya dake Hana Yaduwar Kanjamau, Tarin Fuka da Zazzabin Cizon Sauro da ma’aikatar kiwon lafiya ne suka hada hannu domin gina wadannan wurare a jihar Legas da babbar birnin tarayya, Abuja.

Ya ce gina wannan wuri zai taimaka wajen rage yawan kashe makudan kudade da gwamnati ke yi wajen siyan magunguna a duk lokacin da cutar ta bullo.

Izuwah yace za a kashe dala miliyan 5.1 wajen gina wadannan wurare da zai dauki manyan kwalayen magunguna har 7,680.

Idan ba a manta ba a shekarar da ta gabata ne aka yi karancin magungunan rigakafi na wasu cututtuka saboda gwamnati ba ata iya shigowa da su ba a dalilin rashin wurin adana.

Kammala gina wadannan wurararen ajiya zai taimaka matuka da dazarar an bukaci magani sai dai kawai aje a dauko.

Share.

game da Author