Sanata Akpabio ya fi karfin faduwa zabe -Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa sai jam’iyyar APC ta kwato kuri’un da aka yi zargin an sace wa APC a lokacin zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya a jihar Akwa Ibom.

Buhari ya yi wannan jawabi ne a wani taron ganawa da al’ummar jihar Akwa Ibom, a wata ziyarar godiya da ya je yi dangane da zaben sa da suka yi a zaben shugaban kasa.

PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa jam’iyyar APC ta fadi dukkanin zabukan da aka gudanar a jihar Akwa Ibom.

Ba ta ci kujerar sanata ko ta majalisar tarayya ko daya ba. Haka kuma ba ita ce ta samu kuri’u mafi rinjaye a zaben shugaban kasa ba. Duk PDP ce ta ashe zabukan.

Sanata Godwill Akpabio ya fadi zaben sanata, sai dai kuma ya ce magudi aka yi masa.

APC ta yi ta rakadin cewa ta na neman a cire Kwamishinan Zabe na Jihar Akwa Ibom, Mike Igini.

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya wakilci Buhari a taron ziyarar nuna godiyar jiya Litinin a Uyo, babban birnin jihar Akkwa Ibom, inda ya yi kira ga magoya bayan APC su yi zaben gwamna, kuma su kare kuri’un su.

Osinbajo ya nuna tsananin rashin jin dadin yadda Akpabio ya fadi zaben sanata.

Ya yi zargin cewa INEC ce ta kayar da shi.

Ya yi wa jama’ar jihar alkawarin cewa dukkan kuri’un da aka yi fashi ga Akpabio da sauran ‘yan takara a jihar duk sai an shawo kan matsalar.

“Abin da aka yi wa Akpabio a zaben sanata fashi da makami ne da rana tsaka.
“Ba zai taba yiwuwa Sanata Akpabio ya fadi zabe ba. Ba mu da wata tantama cewa Sanata Akpabio ne ya ci zaben sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

“Ni da Adams Oshiomhole mun fi karfin faduwa zabe. Domin mun dade mu na adawa, don haka ba mai iya sake kayar da mu.
Ya oki jama’a su zabi Mista Ekere, dan takarar gwamna na APC, wanda zai kafsa takara shi da Gwamna Udom Emmanuel na PDP.

APC dai na neman cin zaben gwamnan jigar Akwa Ibom ne, saboda ita da jihar Rivers ce suka fi arzikin danyen man fetur a kasar nan, kuma su biyu ne aka bai wa kason kudade daga gwamnatin tarayya.

Share.

game da Author