Akwai yiwuwar INEC za ta canja jami’an hukumar dake Akwa Ibom da wasu jihohi hudu

0

Wata majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa gwamnatin tarayya na tursasa wa shugaban INEC Mahmood Yakubu ya canja jami’in hukumar dake jihar Akwa Ibom Mike Igini da ma’aikatan hukumar dake wasu jihohi hudu a kasar nan.

Wani ma’aikacin hukumar da ba ya so a fadi sunan sa ya tabbatar da haka wa PREMIUM TIMES ranar Litini a hedikwatar hukumar dake Abuja inda ya kara da cewa hukumar za ta sanar da wannan canji kafin ranar zaben gwamna da na majalisar dokoki na jiha.

” A yanzu haka Yakubu na kokarin kammala shirin canja Igini daga jihar Akwa Ibom zuwa wani jihar duk da cewa yana da masaniya game da matsalolin da haka ka iya kawowa hukumar da sauran zaben da za a yi a kasar nan.

Bayanai sun nuna cewa jam’iyyar APC ne ke bukatan a canja Igini saboda suna zarginsa da aikata magudi a lokacin zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa da aka yi.

Bayanai sun kara nuna cewa shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta canja Igini daga wannan jihar sannan a komar da shi wurin da APC ta amince da shi.

Bayan haka mun sami labarin cewa gwamnati na bukatar Yakubu ya canja jam’ian zaben dake jihohin Ribas, Filato,Benuwai da Imo a dalilin rasa zaben da jam’iyyar APC ta yi a wadannan jihohin.

A yanzu haka jam’iyyar APC ta dakatar da gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha a dalilin mara wa wani dan takaran kujerar gwamna daga wata jam’iyya da yake yi.

Wata majiyar ta kuma bayyana wa PREMIUM TIMES cewa abin takaici ne yadda Yakubu bashi da tsatsaurar ra’ayi irin na tsohon shugaban hukumar Attahiru Jega inda haka ya sa yake bin duk ta inda gwamnati ta karkatashi.

A karshe kakakin hukumar Rotimi Oyekanmi ya karyata duk wani rade radin cewa wai ana takura wa shugaban hukumar Yakubu domin canja ma’aikatan sa dake wasu jihohi a kasar nan.

Share.

game da Author