Kungiyar ‘Better Nigeria Group (BNG), ta goyi bayan matakin da dan takarar zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya dauka na garzayawa kotu, domin kalubalantar nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a kan sa, a zaben 2019.
Kakakin kungiyar mai suna Dickson Iroegbu ne jaddada haka a Abuja jiya Litinin, a lokacin da ya ke wa manema labarai jawabi a Abuja.
Ya ce BNG ta dauki wannan mataki na goyon bayan Atiku din ne bayan da ta tuntubi masu ruwa da tsaki, kuma ta ji kalaman bangarorin jama’a da korefe-korafen su bayan an kammala zabe.
Iroegbu ya ce ba wai don muradin kan sa shi kadai Atiku zai je kotu ba. Ya ce har ma saboda milyoyin ‘yan Najeriya da suka jefa masa kuri’a.
Ya ce idan aka bar hauragiyar da aka yi a lokacin zabe ta tafi a haka, to matsalar za ta iya shafar dimokradiyya nan gaba kadan.
“Mu na kuma yin kira da cewa jama’a su daina kallon wai don Atiku ya je kotu, to ya karya jarjeniyar zaman lafiyar da aka kulla.
“Mu na sane da cewa Atiku na shan matsin lamba daga bangarori da dama cewa kada ya garzaya kotu. Amma kuma mu na so mu shaida wa jama’a cewa idan ba a je kotu din nan ba, to milyoyin wadanda suka jefa masa kuri’a za su ji haushi matuka.”
Buhari ya samu kuri’u milyan 15 yayin da Atiku ya samu milyan 11, waanda shi Atiku ya ce an yi masa magudi kuma gwamnantin tarayya ta yi masa karfa-karfa ta hanyar yin amfani jami’an tsaro.