Dan takaran jam’iyyar PDP Abba Yusuf ya kada gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC a rumfunar zabe dake makarantar firamaren dake Magwan.
Rumfunar zabe uku ne a wannan makaranta masu lambobi kamar haka 056, 057 da 058.
Bisa ga sakamakon Yusuf ya samu kuri’u 76 sannan Ganduje ya sami kuri’u 73 a rumfar zabe 056
A rumfar zabe 057 Yusuf ya samu kuri’u 63 sannan Ganduje ya sami kuri’u 48.
A rumfar zabe 058 Yusuf ya samu kuri’u 76 sannan Ganduje ya sami kuri’u 71
Jumlar kuri’un da Yusuf ya samu ya kai 210, Ganduje ya sami kuri’u 197.