A yau Asabar ne wasu mata a rumfar zabe 010 dake karamar hukumar Ibadan suka kaure da dambe kan rabon kudin da dan takarar kujerar gwamna na jam’iyyar APC Adebayo Adelabu ya bada a sha ruwa.
Shugaban wata kungiyar mata mai suna Iya Emma ta bayyana cewa Kudin da ya shigo hannun ta bai kai Naira 100,000 da sauran matan ke ta cecekuce a kai.
Iya Emma ta kuma yi wa matan tayin cewa kowace mace a rumfar zaben za ta samu Naira 200 daga cikin wadannan kudi da Adelabu ya bada amma matan suka ture wannan tayin cewa Iya Emma ta danne sauran kudin ne kawai domin ta cuce su.
Daga nan sai aka kaure da zage-zage a tsakanin su. Sai ko dambe ya kaure a tsakanin mata inda wasu da aka ba Naira 1000 su raba a tsakanin su suka rincime da naushe-naushe.
Bayanai sun nuna cewa sai da Adelabu ya ba wasu ‘yan jagaliya kudi na cin hanci kafin suka bari ya jefa kuri’ar sa.
Discussion about this post