Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna kuma dan takaran jam’iyyar APC, Nasir El-Rufa’I, Hadiza Balarabe ta yi nasara a rumfar zaben da ta kada kuri’a a Zaben gwamna.
Hadiza ta kada kuri’ar ta a rumfar zabe 001 dake Gwantu I a mazabar Gwantu dake karamar hukumar Sanga.
Sakamkon zaben ya nuna cewa Hadiza ta sami kuri’u 150 sannan dan takarar jam’iyyar PDP ya sami kuri’u 50.
A sakamakon zaben majalisar dokoki na jihar APC ta samu kuri’u 140 sannan jam’iyyar PDP 58.
Idan ba a manta ba gwamnan El-Rufa’I ya maya gurbin mataimakinsa Barnabas Bantex da Hadiza ne bayan shi Bantex ya nemi ya yi takarar sanata na yanki Kaduna ta tsakiya.
Bantex ba iya yin nasara ba domin kuwa Danjuma Laah na Jam’iyyar PDP ne ya lashe Zaben wannan yanki.