A bayanan da jam’iyyar PDP ta mika a gaban kotu ranar Laraba, siun nuna cewa na’urar tattara sakamakon zabe na hukumar INEC ya nuna jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben shugaban kasa da kuri’u miliyan 1.6.
Wannan daya ne daga cikin hujjoji 50 da jam’iyyar PDP ta mika a gaban kotun dake sauraron shari’ar zaben shugaban kasa da a Abuja.
Idan ba a manta ba tun bayan bayyana sakamakon zaben shugaban Kasa da hukumar zabe tayi jam’iyyar PDP ta yi watsi da wannan sakamako cewa jam’iyyar APC ta tafka magudi a zaben.
A sakamakon da aka bayyana bayan zaben, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da kuri’u 15,191,847 inda Atiku ya samu kuri’u 11,262,978.
A bayanan korafin da PDP ta mika, ya nuna cewa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben da kuri’u 18,356,732 inda ya kada Buhari na Jam’iyyar APC da ke da kuri’u 16,741,430.
Bayan nan PDP ta ce takardan kammala jarabawar makarantan sakandare da Buhari ya mika ta boge ne domin a cewar su a lokacin babu jarabawar WASC, amma kuma ita Buhari yake gadara da.
Haka kuma lauyan Atiku da Jam’iyyar PDP ya mika wa kotu shaidar takardun watardun da aka shigar da sakamakon zabe, da wasu bayanai dake nuna yadda aka yi magudi da a wajen hada alkalumma sakamakon zaben da wasu bayanai.
Discussion about this post