KIDAYAR KURI’UN BAUCHI: Kotu ta daga karar da Gwamna Abubakar ya kai INEC

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta dage sauraren karar da Gwamna Mohammed Abubakar na Jihar Bauchi ya kai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC.

Abubakar ya gurfanar da INEC ce a kotu, tare da kalubalantar yadda hukumar ta canja shawarar sake kidaya kuri’un Karamar Hukumar Tafawa Balewa, maimakon zaben da ta ce za ta sake a wuraren da ake tankiya.

Abubakar ya na mai cewa tunda dai har Babban Jami’in Zabe na Jihar Bauchi, Mohammed Kyari, ya sanar da cewa zabe bai kammalu ba, to INEC ba ta da hurumin da za ta ce zabe ya kammalu, za ta sake kidaya kuri’u kadai.

Mai shari’a Inyang Eko, wanda a jiya Talata ya dakatar da ci gaba da kidayar kuri’un da INEC ta ce za ta ci gaba da yi a jiya din, a yau kuma ya dage shari’ar zuwa ranar 21 Ga Maris, 2019.

Dage shari’ar ya biyo bayan rokon da lauyan jam’iyyar APC, wadda itace jam’iyyar gwamna Abubakar ya yi cewa an turo masa raddin INEC a makare, don haka ya na rokon ta dan ba shi ‘yan kwana daya ko biyu da zai samu damar yin nazarin su.

JULA-JULA DAGA TAFAWA BALEWA ZUWA KOTU

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bayar da hukuncin dakatar da ci gaba da kidayar kuri’un ne bayan mai kara, wato Gwamna Abubakar ya nemi a hana INEC ci gaba da kidayar da ta ce za ta yi, maimakon zaben da ta ce za ta sake a wasu mazabar, kamar yadda ta hakkake a baya.

Ekwo ya aika sammacin dakatar da kidaya har sai ya gama sauraren karar da Abubakar ya shigar tukunna.

PDP TA SHIGA CIKIN RIGIMAR

A halin yanzu kuma a safiyar yau Alhamis ce kuma jam’iyyar PDP ta nemi kotun da ta tsoma ta cikin wadanda ke da ruwa da tsaki a rigimar shari’ar zaben jhar Bauchi.

Baya ga wannan kuma jam’iyyar PDP har ila yau ta kai karar Mai Shari’a Ekwo a gaban Hukumar Kula da Alkalan Najeriya, inda ta nemi a hukunta shi, saboda ya yi riga-malam-masallacin umarnin hana INEC yin aikin da doka ta wajabta mata, wato ci gaba da kirga akwatunan zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa.

Haka Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Ologbodiyan ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Laraba.

PDP ta ce haramun ne alkalin ya amince da ci gaba da sauraren shari’ar, wadda Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ce kadai ke da ikon sauraren shari’ar.

Share.

game da Author