MATSALAR MAHARA: Gwamna Masari ya kai kuka ga Osinbajo

0

Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina ya ce ya na ganawa da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da kuma shugabannin hukumomin tsaro, dangane da yawaitar hare-haren samame da garkuwa da mutane da suka addabi jihar Katsina.

Masari ya bayyana haka a lokacin da ya ke masa tambayoyin manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, bayan ya gana da Osinbajo.

Ya ce ya je fadar ce har da dalilin taya Osinbajo murnar lashe zaben 2019 da APC ta yi.

Kafin na bar Abuja na koma Katsina, zan gana da Babban Sufeto Janar a ‘Yan Sanda da kuma Babban Darakta Jami’an DSS.

Ina so za mu kara tattauna matakan tsaron da za a kara dauka domin kara karfafa tsaron da a yanzu jami’an sojoji ke yi da wanda sauran wadanda abin ya shafa ke bayarwa.

Da ya ke magana a akan zaben sa, ya ce ya cika alkawurran da ya dauka a kamfen din zaben 2015, shi ya sa al’ummar jihar Katsina ta sake zaben sa.

Jihar Katsina ta fada cikin mummunan halin rashin tsaro a kananan hukumomi kusan goma. A zaman yanzu ana tsare da Alaramma Ahmad Sulaiman, kusan mako daya kenan a cikin jihar.

An kama shi makonni biyu bayan yin garkuwa da mahaifiyar matar Gwamna Masari.

Har cikin babban birnin jihar ake shiga a dauke mutum a yi garkuwa da shi.

Share.

game da Author