Wadanda suka yi garkuwa da Alaramma Ahmad Sulaiman, sun nemi a bisa su diyyar naira miliyan 300 kafin su sake shi.
An kama fitaccen malamin mai karatun Alkur’ani a jihar Katsina a lokacin da ya ke komawa garin su Kano, daga jihar Kebbi.
An kama shi ne a tsakanin Sheme da Kankara, cikin jihar Katsina, a ranar Alhamis da ta gabata.
Tsautsayin kamun ya fada kan sa ne kwana daya tal kafin daurin auren ’ya’yan sa uku da aka shirya zai aurad da su washegari Juma’a a gidan sa, a cikin Kano.
Kamar yadda Jaridar PR ta wallafa, wata muryar daya daga cikin maharan da suka kama shi da ake ta watsawa a soshiyal midiya, ta nuna yadda ake tattauna batun sakin na sa da wani da ya ce ya na magana ne a madadin iyalan malamin.
Baya ga shaharar da Sheikh Ahmad Sulaiman ya yi wajen karatu a wa’azin kungiyar Izala bangaren Kaduna, sannan kuma ya yi suna a zaben 2019, inda ya rika sheka addu’o’i a kan Shugaba Buhari na APC ya samu nasarar lashe zabe a kan abokin takarar sa, Atiku Abubakar na PDP.
Daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da malamin ya ce su ba garkuwa da shi suka yi niyyar yi tun da farko ba.
Ya ce kwangilar kashe shi aka ba su, kuma sai da aka ba su naira milyan 300 kafin su tare shi a kan hanya su kama shi.
Ya ce tun daga Kebbi su ke bin sa. Wani babban dan siyasa ne ya ba su kudi domin su kashe shi.
Dan bindigar ya ce an shaida musu cewa Ahmad Sulaiman dan ta’adda ne, don haka su kashe shi.
Amma yayin da suka kama shi, sun fahimci ba dan ta’adda ba ne, shi ya sa ba su kashe shi ba.
Daga nan sai ya ce abin da suke so, kawai a biya su naira milyan 300 da suka karba daga hannun wanda ya ba su aikin kashe malamin, sai su maida masa abin sa. Ya ce tunda ba su kashe malamin ba, to tilas su maida kudi ga wanda ya ba su kudi domin su kashe shi.
“Idan ba za ku biya ba kuma, to za mu kashe shi, kuma mu je wurin wancan mutumin ya cika mana abin da ya yi alkawari idan mun aikata abin da ya ke so mu aikata din.” Inji dan bindigar wanda furucin kalaman sa sun tabbatar da cewa Bafulatani ne, duk kuwa da cewa da Hausa su ka rika yin magana.
Sai dai a tsawon lokacin da wanda ke tsare da malamin ke waya da daya daga cikin na hannun damar malamin, an nemi a yi magana da Malam Sulaiman ta waya, sai ya ce ba ya kusa da inda suke tsare da malamin a wancan lokacin da suke wayar.
CIKIN WATA MURYAR
A cikin wata muryar da aka rika yadawa a soshiyal midiya main tsawon minti uku kuma, an rika jin yadda Malam Sulaiman ke rokon wanda suke waya, ya na umartar sa da a sayar da gidajen sa na Kano domin a kubutar da shi daga hannun maharan da suka tsare shi.
Kuma za a ji ya na sanar da cewa a sanar da su Kabiru Gombe da Bala Lau da Gwamnan Jihar Kebbi da Gwamna Masari na Katsina halin da ya ke a ciki.
Kamar Zamfara, ita ma Jihar Katsina ta zama sansanin masu garkuwa da mutane, inda satar jama’a ta yi kamari a Kananan Hukumomin Jibia, Dandume, Faskari, Sabuwa, Danmusa, Safana, Kankara, Batsari, Dutsinma, Kurfi, Funtua da cikin birnin Katsina.
A lokacin da aka sace Ahmed Sulaiman, masu garkuwa da mutane na ci gaba da tsare da surikar Gwamnan Jihar Katsina, wadda aka sace a cikin garin Katsina, a gidan ta da ke cikin GRA, Katsina.
Amma rahotanni sun ce an sako ta bayan ta shafe kwanaki da dama a tsare.
Idan ba a manta ba, watannin baya ma an yi garkuwa da ‘yan agaji na Kungiyar Izala su 20 a cikin Jihar Katsina, bayan sun dawo daga wa’azi na Kasa a Jihar Sokoto.