Kotu ta daure birkilan da ya yi wa matar aure fyade a gidan ta

0

Kotun majistare dake jihar Kano ta yanke wa wani birkila mai suna Abdulrazak Dahiru dake da shekaru 30 hukuncin zama a kurkuku bayan kama shi da laifin dannne wata matan aure da karfin tsiya.

Lauyan da ya shigar da karar Muhammad Bakori ya bayyana cewa Dahiru ya aikata wannan ta’asa ne ranar 25 ga watan Janairu da karfe 12 na rana a kwatas din Dorayi Unguwar Amare.

Bakori ya ce Dahiru ya shiga dakin matan ne dauke da wuka da igiya bayan ya tabbatar mijinta baya nan.

” Bayan Dahiru ya yi mata barazanar zai kashe ta sai ya daureta da igiya, ya cusa tsumma a bakinta sannan ya danne ta.

” Bayan ya gama sai ya dauke wayar ta da kuma kudi har Naira 20,000.’

Dahiru bai amsa laifin sa ba.

Alkalin kotun Fauziyya She-She ta yanke wa Dahiru hukuncin zama a kurkuku sannan ta daga shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Maris.

Share.

game da Author