Da zaran an ambaci sunayen wasu ‘yan siyasa a Kaduna, idan har kana siyasa to sai kaji gaban ka yayi ras musamman idan ba ra’ayin ku daya bane da irin wadannan ‘yan siyasa a jihar.
A karon farko a tarihin siyasar Kaduna an kawo lokacin da kusan duka wadanda ke ji sune masu fada aji sannan ke iya karkato da ra’ayin jama’ zuwa ga abin da suke so a siyasa sun sha kasa, tarin su a wuri daya bai yi wa dan takarar su tasiri ba ko kuma jam’iyyar PDP a jihar.
Jiga-jigan ‘yan siyasa kamar su Sanata Suleiman Hunkuyi, Sanata Ahmed Makarfi, wanda tsohon gwamna ne a jihar sannan wanda jam’iyyar PDP ke bugun kirji da a jihar duk ba su yi mata rana ba.
Tsakanin Hunkuyi da El-Rufai
Shi dai Suleiman Hunkuyi an san shi a jihar Kaduna da iya shirya tuggun siyasa. Duk wani dan takara a jihar Kaduna sai ya jingina da shi ko ta halin kaka idan dai yana so yayi tasiri a siyasan Kaduna.
A lokacin da El-Rufai ya fito takara tuni suka hada kai da Hunkuyi domin su iya kada gwamna mai ci a wancan lokaci wato Ramalan Yero na jam’iyyar PDP.
Duk da cewa Hunkuyi tare da El-Rufai sun hada kai domin samun nasara a zaben 2015, an fi yi wa siyasar wannan lokaci da lakabi da goguwar Buhari ce sila.
A 2015, ko da wa kake tare da muddun kana jam’iyyar Buhari wato APC, tabbas zaka yi nasara a zaben.
Ana ta tafiya rumui-rumui kwatsam sai rashin jituwa ya kunnu kai a tsakanin El-Rufai da Hunkuyi. Hakan ko ya faro ne tun bayan zaben wakilan jam’iyyar da aka yi inda bangaren Sule Hunkuyi, Shehu Sani da sauran su suka koka cewa an yi musu karfa-karfa a zaben wakilan.
Tun daga wannan rana aka ja daga, ba a ga maciji tsakanin Sule Hunkuyi da Gwamna El-Rufai.
Abin ya kai ga har rusa masa gida aka yi wanda ofishin kamfen din sa ne a dalilin cewa bai mallaki takardun kwarai ba na jam’iyyar wannan fili.
A haka ne dai jam’iyyar APC ta gagari Hunkuyi zama a cikinta, ya tattara nasa-ina-sa ya koma gidan sa ta da wato jam’iyyar PDP.
A nan kuma suka fara shirya yadda zasu kada gwamna mai ci a jihar Kaduna wato El-Rufai ko ta halin kaka.
Tsakanin El-Rufai Da Jam’iyyar PDP
Komawar Hunkuyi jam’iyyar PDP ke da wuya sai suka hade da wasu jiga-jigan jam’iyyar kamar Sanata Makarfi, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, da wasu da dama ‘yan jam’iyyar domin fafatawa da El-Rufai a zaben 2019.
Tun daga wannan lokaci El-Rufai da babban mai bashi shawara kan harkar Siyasa, Mal Uba Sani suka koma teburin sake lissafin yadda zasu yi gaba da gaba da gungun ‘yan PDP da suka rantse sai sun ga bayan su.
Tafiyar sai ta canja salo, aka fara kamfen kamar ba gobe. Gogan naka kuwa, wato El-Rufai, ya cigaba da caccakar ‘yan adawar sa kamar ba zabe ne zai tunkara ba.
Zaben 2019
Duk da cika bakin da gwamna Nasir El-Rufai ya rika yi tun kafin zaben har zuwa ranar zabe, jam’iyyar PDP ba ta iya tabuka komai ba musamman a yankin Arewacin Kaduna. Domin kuwa El-Rufai gida-gida ya bisu yana dokewa daya bayan daya.
Tarin Sule Hunkuyi, Ahmed Makarfi, da shi kan sa Isah Ashiru dan takarar gwamnan jihar a PDP ba su iya kawo koda karamar hukuma daya bace a wannan yanki ta shiyyar Kaduna ta Arewa.
Yankin kudancin Kaduna ne kawai suka iya yi wa jam’iyyar PDP halasci inda suka kawo duka kananan hukumomin da ke wannan yankin. Kama daga ‘yan majalisun jiha ne zuwa wadanda suka tura Abuja.
Makarfi kuwa, a matsayin sa na jagoran PDP a jihar Kaduna bai iya kawo wa PDP karamar hukumar sa ba. Haka shima Hunkuyi duk da cika bakin da ya rika yi cewa shine ya tallata El-Rufai, kuma shine zai tsige shi a gwamnan jihar Kaduna, ba Kaduna ba, karamar hukumar sa ta Kudan ma bai iya kawo ta ba.
Namadi Sambo, wato tsohon mataimakin shugaban kasa, shima bai yi wa jam’iyyar PDP rana ba a zaben 2019, ko da ko ta kujerar dan majalisa ne.
Shin ko El-Rufai ya zama gogan siyasar Kaduna daga yanzu ko A’a ?
Discussion about this post