Yayin da jam’iyya mai mulki, APC ta dakatar da Gwamna Rochas Okorocha har sai yadda hali ya yi, bisa laifin goyon bayan dan takarar gwamna na wata jam’iyya, ta ce ba za ta hukunta Amaechi ba saboda aikata irin laifin Okorocha da ya yi.
APC ta ce abin da Amaechi ya yi ba daidai ya ke da abin da Okorocha ya tafka ba.
A jihar Imo, Okorocha ya goyi bayan Uche Nwosu, dan takarar gwamnan AC, maimakon ya goyi bayan Hope Uzodinma, dan takarar APC.
Hakan ya janyo Nwosu da Uzodinma duk sun fadi zabe, inda Emeka Ihedioha na PDP ya kayar da su.
Sai dai shi Okorocha ya ci zaben sanata a karkashin APC, amma har yau ya na ta jekala-jekala, domin INEC ta hana shi takardar shaidar cin zabe, a bisa ikirarin da jami’in ta mai bayyana sakamakon zabe ya yi cewa tilasta shi aka yi ya bayyana cewa Okorocha ne ya ci zabe, alhali ba shi ya ci ba.
A jihar Ribas kuwa, Kotun Koli ta haramta wa APC shiga zabe. Sai bangaren APC mai goyon baya daga Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya goyi bayan dan wata jam’iyya, AAC, wato Biokpomabo Awara a matsayin dan takarar gwamnan da za su zaba.
A jihar Ribas dai da yawa ba su ma san dan takarar ta AAC da ita kan ta AAC din ba, sai ana kwanaki bai fi uku ba kafin a yi zaben gwamna.
A kan haka ne Kakakin APC Lanre Issa-Onilu ya ce Amaechi bai karya dokar jam’iyyar APC ba, kuma bai yi wani laifi ga jamiyyar ba.
“Duk wani abu da ya faru a jihar Ribas, kuma duk wani abu da Amaechi ya yi, daidai ne, jam’iyyar mu ta yarda da dukkan matakan mara wa dan takarar AAC da ya yi.” Inji Onilu.
Daga nan sai ya kara da cewa har yanzu Okorocha ya na nan a matsayin wanda jam’iyya ta dakatar.
Ya kuma kara da cewa APC babu yadda za ta yi ta sa baki a bai wa Okorocha satifiket na cin zabe, tunda INEC ta ce an tilasta wa jami’in ta bayyana Okorocha a matsayin dan takara.
Sannan kuma APC ta ce har zuwa yanzu a matsayin dakatacce daga jam’iyyar ya ke.
Discussion about this post