Majalisar Zartaswa ta amince da bukatar Karamin Ministan Harkokin Man Fetur, Ibe Kachikwu ya gabatar mata, inda ya nemi amincewar ya kashe zunzurutun kudi har naira biliyan 1.4 wajen zanen fasalin ofishin Hukumar Kula da Man Fetur, wato DPR.
Wadannan makudan kudade dai ba wai a ginin ofishin za a kashe su ba. Za su shige ne wajen biyan ladar zanen taswirar ofishin a kan takarda kawai.
Kachikwu ya ce zanen ba karamin aiki ba ne, domin za a zana bene mai hawa 12, wanda ya ce tuni aka ba wani kamfanin Najeriya kwangilar zanen ofishin a kan takarda, domin a ga yadda zai kasance idan an gina shi.
Da ya ke wa manema labarai jawabi bayan kammala taron majalisar jiya Laraba a fadar shugaban kasa, Kachikwu ya ce gwamnati ta yanke shawarar gina sabon ofishin hukumar a Abuja, ta yadda bayan an kammala, za a rabo shi daga Legas zuwa Abuja.
‘Yan jarida sun tambayi Kachikwu cewa ba ya ganin wadandan makudan kudade sun yi yawa, tunda ba a ginin za a kashe su ba, a kan ladar biyan zanen taswirar ginin za a kashe su?
Kachikwu ya amsa da cewa ai ginin ofishin zai lashe naira biliyan 35 cur.
A taron kuma an amince da bukatu uku da Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya kai gaban Majalisar.
Ya kai takardun neman yin wasu ayyuka uku a ofishin NTA, NAN da FRCN.
An amince a kashe naira milyan 293 domin sayen kyamarori, makirho da talbijin a NTA.
An kuma amince a kashe naira miliyan 148 wajen sayen motoci samfurin Fijo har 15 ga ofishin NAN.
Na uku kuma shi ne aikin sayen taransimita mai karfin 10kw har guda 12 ga Gidan Radiyon FRCN, wanda zai ci sama da naira miyan 540. Sannan kuma za a kashe naira miliyan 311.6 domin sayen motocin hadawa kai-tsaye da dauko rahotanni.