TAMBAYA: Mene hukuncin wanda yana Jin Kiran sallah Amma kafin ya tashi an idar sai yayi shi kadai?
AMSA: Alhamdu-lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Wajibin Musulmi ne halartar Masallaci domin Sallar Jam’i, mutumin da ya bar gidansa cikin alwala zuwa masallaci, Allah yana daga darajarsa
duk taku daya, kuma yana kankare masa zunubi duk taku daya, Mala’iku suna masa addu’ar gafara da rahama da tsira da zarar ya shiga
masallaci har sai ya fito. Wannan garabasa ce da bai kamata musulmi yayi sakaci da shiba.
Wajibe ne musulmi ya kiyaye lokutan Sallah kuma ya dinga kirdadonsu da tsaresu, amma idan lokaci ya kwace masa ko ya shafa’a ko wani uzuri ya bijiro masa kamar na barci, to babu laifi idan bai samu jam’i a masallaci ba, matukar hakan bai zamo masa jikiba.
Lallai Sallar Jam’i a masallaci tana da daraja ashirin da bakwai akan Sallar mutum daya, idan mutum yayi Sallar shi kadai ba tare da
uzuriba, wasu malamai na cewa ba shida Sallah kuma idan kasalace ko son zuciya ta hana shi zuwa masallaci, to ya zamo Munafiki ko Mai
bautawa son zuciyar sa.
Hukuncin duk wanda yaji kiran Sallah to ya amsa, ya halarci masallaci, ya sallaci abinda ya riska, ya rama abinda ya kubuce masa, domin
sallar jam’i a masallaci wajibe ne, idan ba a yita a masallaci ba, to Malamai sun ce babu ladar darajar jam’i ashirin da bakwai. Kuma sun ce wanda yayi shi kadai a gida batare da uzuriba, ya yi zunubi da sabawa umurnin Allah, idan hakan kuma ya zamo masa jiki to zai iya shiga
cikin munafukai. Ibn Abbas ya ce an tambayi Annabi SAW akan wani musulmi mai yawan azumi da sallar dare amma baya zuwa jam’i a masallaci, Annabi SAW yace dan wuta ne.
Ba bu jam’i sai a masallaci, ba bu Sallah sai a masallaci: Allah yace: ku tsaida Sallah kuma kubada zakka, sannan ku yi Sallah da masallata (Al-Bakara 43), A cikin dakunan (masallatai) da Allah yayi umurne da a daukakasu, ana ambaton Allah a cikinsu safe da yamma (An-Nur 36).
Hadisi ya inganta Annabi SAW ya ce: duk wanda ya ji kiran Sallah, bai je masallaci ba, to ba shida Sallah, saidai mai uzuri. Ibn Abbas ya ce Uzuri shi ne tsoro ko rashin lafiya. Ibn Mas’ud ya ruwaito cewa Annabi SAW ya ce: duk musulmin da ke son haduwa da Allah gobe kiyama yana mai farin ciki, to ya tsare wadannan salloli a lokacin da a ka kira Sallah. Allah ya shar’antawa Annabinku hayoyin shiriya, kuma lallai su (Salloli) ne hanyoyin shiriyar, idan kuka yi sallolin ku agida, to kun bar Sunnar annabin ku, kuma idan kuka bar Sunnar annabin ku to kon bace, hakika babu mai kin zuwa jam’i sai munafiki…. (Muslim)
Musulmai masu Sallah a gida, da office da sauran guraren da ba masallatai ba ne, to su ji tsoron Allah, kowa ya je masallaci.