Ana shirin kara yawan kuri’un da aka soke a Bauchi domin a kada PDP da karfin tsiya – PDP

0

Jam’iyyar PDP ta koka kan yadda ake kokarin kokarin ganin ana kara yawan kuri’un da aka soke a jihar Bauchi don ko ta halin Kaka a kada dan takaran jam’iyyar, Bala Mohammed.

Kakakin jam’iyyar PDP na kasa Kola Ologbondiyan,ne ya bayyana haka inda ya kara da cewa a bayanan da suka samu, wasu jami’an hukumar zabe sun hada kai da jam’iyyar APC domin kara yawan kuri’un da aka soke domin aba jam’iyyar daman yin magudi.

” Muna sane kuma mun samu sahihan bayanai kan yadda ake kokarin yi mana murdiyya ko ta halin kaka a jihar Bauchi. Mun gano wai za a kara yawan kuri’un da aka soke daga 70,000 zuwa 184,555 domin ba APC daman yin murdiyya ko ta halin kaka.

” Mun samu bayannan irin miliyoyin kudin da aka rika dankarawa jami’an hukumar zaben don su tabbata sun murde zaben jihar Bauchi. Mutanen jihar Bauchi sun zabi abin da suke so idan aka nemi a canja musu zabin su ba za su yarda ba.

Idan ba a manta ba an bayyana cewa zaben gwamna bai kammalu ba a jihohin Bauchi, Kano, Adamawa, Sokoto, Benuwai da Filato a dalilin samun yawan kuri’un da aka soke a lokacin zabe.

Wadannan kuri’u sun fi yawan ratar da jam’iyyyn da suka yi nasara suka ba wadanda suka kada.

Ana ta korafe-korafe game da wannan salo na rashin kammala zabe da aka bayyana a jihohin da ake ganin duka jam’iyyar PDP ce ke kan gaba.

A cikin wadannan jihohi, jihar Filato ce kawai ta fado cikin jerin wadannan jihohi da jam’iyya mai mulki ce ke mulki a jihar.

Share.

game da Author