TAMBAYA: Musulmi na gadon Wanda ba Musulmi ba? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Musulmi na gadon Wanda ba Musulmi ba? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.

Abubuwa uku ne ke hana gado a musulunce: kisa, wato mutum ya kashi wanda zai gada, ko bauta, bawa baya gado, da shi bawan da abinda ya mallaka duk na mai gidansa ne, abu na ukun kuwa, shi ne bambancin addinin magada. Tambayarmu ta yau ita ce: shin Musulmi na gadon Wanda
ba Musulmi ba?

A musulunce bambancin addini ya haramta gado tsakanin ‘yan uwa.

Musulmi ba ya gadon danuwansa wanda ba Musulmi ba. Kamar yadda Kafiri ba zai gaji dan uwansa Musulmi ba. Idan wanda ba Musulmi ba ya mutu,to ‘yan uwansa Musulmi ba za su gaje shi ba, kamar yadda ba za su gaje shi ba.

Bambancin addini tsakanin ‘yan uwa ya haramta gado tskanin ‘ya’ya, ma’aurata, iyaye, kanni, yayyi da duk sauran ‘yan uwa da makusanta.

Hadisai ya indanta daga Annabin Rahama cewa “Musulmi baya gadon Kafiri, kuma Kafiri baya gadon Musulmi”, “ Babu gado tsakanin mabambanta addini”.

HUKUNCIN GADON MABAMBANTA ADDINI A MUSULUMCI

1. Musulmi bai gadon Kafiri, ko kirista, ko Bayahude, ko arne da duk wanda ma ba Musulmi ba ne. Suma kuma babu mai gadonsa. Wasu daga cikin magabata, kamar Mu’azu, Mu’awiyya da Sa’idu Ibn Musayyib sunada ra’ayin cewa Musulmi na iya gadon dan uwansa wanda ba musulmiba. Sun dogara da wasu hujjoji wanda duk malamai suka ce masu rauni ne.

2. Amma babu bambancin addini tsakanin duk wanda ba musulmi ba, wato Kafirai, ko Kiristoci, ko Yahudawa, ko Arna, duk daya suke. Don haka su za su kaji junansu. Domin kafirci tafarki daya ne. Amma wasu daga cikin magabata sunada ra’ayin cewa babu gado tsakaninsu harsai
addininsu ya zama daya.

3. Idan Musulmi ya rasu, kuma duk ‘yanuwansa kafirai ne, to ba za su gaje shi ba, duk dukiyarsa ta Baitul-Mali ne. Domin kafiri baya gadon Musulmi. Kamar yadda musulmai ba za su gaji danuwansu kafiri ba, ko da kuwa duk ‘yan uwansa Musulmai ne.

4. Imam Ahmad yana da ra’ayin cewa: idan kafiri ya Musulunta bayan mutuwar dan uwansa Musulmi, amma kafin a raba gado, to ana iya raba gadon da shi. Wannan kofa ta rabon gado da shi, tana iya sashi yayi kwadayin Musulunci, kuma ya musulunta.

5. Musulmin da yayi Ridda (Murtaddi) baya gado kuma ba a gadonsa. Wato
babu wanda zai gaje shi duk duniya daga cikin ‘yan uwansa Musulmai, Kiristoci, Yahudawa ko Arna. Kuma shima ba zai gaki kowa ba a duniya.

ALLAH SHI NE MAFI SANI.

Share.

game da Author