Yadda Gwamnatin Buhari ta yi wa gangamin PDP na Abuja kafar-ungulu

0

Jam’iyyar PDP ta nuna bacin ran ta bayan sanarwar dage babban gangamin kamfen din da ta shirya yi a jiya Asabar a Abuja.

Wata sanarwa da kakakin yada labarai na PDP, Kola Ologbondiyan ya fitar a jiya, ya ce PDP ta dage taron ne bayan da gwamnatin tarayya ta hana su gudanar da taron dan takarar shugabancin kasa, Atiku Abubakar, a tsohon filin fareti na kasa.

Kakakin ya kara da cewa wannan rashin adalci da gwamnatin Buhari ke yi wa ‘yan adawa, ya na nan a rubuce, kuma akwai ranar kin dillanci.

Ya ce PDP ta rigaya ta biya kudin yin amfani da filin, kuma an karbi kudin ta. Amma daga baya sai aka kawo wani dalili daban.

Kola ya ce tun farko a Legas PDP ta yi nufin shirya gamgamin, amma sai gwamnati ta ce ba zai yiwu ba, domin a ranar Asabar din ce Shugaba Buhari zai je na sa kamfen din a Legas.

Idan ba a manta ba, jama’a sun rika kukan rashin adalci yayin da gwamnatin PDP ta rika hana APC taruka a filayen kwallo.

Kan haka Buhari ya yi alkawarin cewa idan ya yi nasara zai yi adalci domin filin wasa na kowa ne, ba na jam’iyya mai mulki ba ce kadai.

Sai dai kuma gwamnatin Buhari ta hana Sanata Rabiu Kwankwaso taron kaddamar da yakin neman zaben sa cikin Satumba, 2018, da ya yi niyyar yi a Dandalin Eagle Square.

Amma kuma PDP na sanar da cewa ta na sa ran taron na Abuja zai yiwu a ranar Talata mai zuwa.

Share.

game da Author