Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB), ta jaddada cewa ba za ta kara wa’adin yin rajistar rubuta jarabawar shiga jami’a, wato JAMB ta shekarar 2019 ba.
Shugaban Hukumar Gudanarwar JAMB, Emmanuel Aguzie, ya bayyana haka a wani rangadin da ya yi a Legas, na duba cibiyoyin da ka bude domin yin rajistar JAMB.
Aguzie ya ce hukumar na nan kan bakan ta cewa za a rufe yin rajistar a ranar 21 Ga Fabrairu.
Ya ci gaba da cewa naira 4,700 kacal ne kudin rajista, kuma an hana zuwa ‘business centre’ a yi rajista.
Ya ce dalilin haka ne ya sa ko ina aka bude cibiyoyin da dalibai za su je su yi rajista kai tsaye.
Ya kara da cewa ya gamsu da yadda tsarin yin rajistar ke tafiya, kuma za a zauna yin jaranawar ce a ranar 16 Ga Mayu.
Discussion about this post