TUGGU: Yadda sojoji suka so hargitsa zaben 2015

0

PREMIUM TIMES ta bankano wani tuggu da gungun wasu sojoji suka kulla da nufin harrgitsa zaben 2015, sai dai hakar su ba ta cimma ruwa ba.

Hakan kuwa ya faru ne yayin da uku daga cikin sojoji hudun da aka ba aikin hargitsa zaben suka rika bi su na warware kullin tuggun da suka shuka, domin kada mugun shirin ya yi nasara.

A zaben shugaban kasa na 2015 a Jihar Barno aka kulla tuggun.

Dama kuma PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda wasu manyan jami’an sojoji suka bayar da umarnin a harfar da yamutsi domin a kasa bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a Jihar Barno.

Binciken da wannan jarida ta shafe shekaru biyu ta na gudanarwa, ta bankado cewa yayin da sojoji suka ga cewa sakamakon zaben ya fara nuna cewa Goodluck Jonathan ba ya kan nasara, wasu manyan jami’an sojoji sun tashi haikan da nufin hana bayyana sakamakon zaben Jihar Barno.

Sun kuma yi kokarin haddasa yamutsi a Maiduguri domin kawo tsaiko ko cikas a zaben a cikin Maiduguri.

Shirin da su ka kulla din kuwa, ya na nufin hargitsin da zai tashi a Maiduguri, zai fantsama zuwa sauran sassan kasar nan, ta yadda Shugaban Kasa na lokacin Goodluck Jonathan zai kakaba dokar-ta-baci, kuma a Kano tsaida bayyana sakamakon zabe.

ZARATAN ‘YAN TUGGU HUDU

Su ne Manjo Janar Lamidi Adeosun, Burgediya Janar Hamisu Hassan, Kanar Danladi Hassan, Kanar Mohammed Sulaiman. Su ne aka bai wa aikin shirya yadda za a dagula harkar zaben gaba daya.

Sai dai kuma sojojin sun ji tsoron abin da zai iya biyo baya a fadin kasar nan, wannan ya sa su ka shirya tuggun yadda zai yi nasara. Haka binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar.

Dukkan wadannan sojoji da aka lissafa a sama, su na rike da manyan mukamai ne a rundunoni da sansanonin sojoji daban-daban a Maiduguri a lokacin.

Wasu muryoyi da aka yi rikodin, kuma a yanzu haka PREMIUM TIMES ya mallake su, sun tabbatar da shaidar yadda Adeosun, Hassan da Sulaiman su ka bagarar da hedikwatar sojoji a Abuja, suka kitsa musu tuggun da idan an yi shi ba za a yi nasarar hargiza zaben ba.

Sai dai kuma har yau ba a san wanda ya yi rikodin din ba, amma dai tabbas an damka wa Shugaba Muhammadu Buhari muryoyin su tun a cikin watan Yuni, 2016.

‘MUGU SHI YA SAN MAKWANTAR MUGU’

Daga cikin tattaunawar da sojojin suka rika yi, akwai inda Kanar Hassan ya ke nuna cewa a ofishin INEC Na Maiduguri duk dandazon matasan APC ne suka yi dafifi, wasu ma kwance su ke a kan siminti.

Ya ce wa Sulaiman babu abin da za a iya yi a wurin, sai dai fa idan matasan PDP za a cinna musu a wurin, su ma su je su yi dafifi.

An jima rika jin yadda Kanar Hazzan ke bada labarin duk halin.da jami’an INEC na Maiduguri me ciki kafin su bayyana sakamakon zabukan majalisar tarayya da na sanatoci.

Ya kuma rika bayyana wa hedikwata cewa hatta wayar kwamishinan zabe na Jihar Barno ya kasa samuwa a waya, domin kashe ta ke.

“To a halin yanzu dai ofishin INEC babu kowa, sai ‘yan sanda masu tsaro da kuma wasu tsirarun matasa. Da a ce mun samu ganin Kwamishinan Zabe, ai da mun haddasa yamutsi a wurin.”

Adeosun: Ka san haka ba zai yiwu ba fa. Ta ya za mu je wurin mu haddasa barkewar tashin hankali, alhali hana tarzoma ne aikin mu?”

Kanar Sulaiman: Yallabai ai Kanar Hassan ba ma zai iya shiga ofishin INEC ba, saboda akwai matasa. Za su yi masa kallon dan majalisar tarayya ne na PDP. Akwai kuma kyamarorin daukar hoto birjik. Sannan kuma mu dubi abin da wannan yamutsin zai iya haifarwa nan gaba.

Manjo Janar: Wannan haka ne kam ba yau kadai za mu yi la’akari ba, har da gobe.
Daga nan kuma an rika jin yadda Major Janar Adeosun, Kanar Sulaiman da Kanar Hassan suka rika kulla bayanai na karya da za su fada wa ogogin su a hedikwatar sojoji a Abuja, domin su gamsu kamar kulle-kullen da aka ce su yi ba tafiya daidai.

Sun rika tattauna yadda za su yi musu karyar cewa sun damke kwamishinan zabe, kuma sun cafke farfesan da zai bayyana sakamakon zabe, alhali kuwa ba su kama kowa ba, na su so Najeriya ta hargitse.

Adeosun, Hassan da Sulaiman sun kuma tattauna yadda za su rika shaida wa manyan na su cewa komai na tafiya daidai, har sai a karshe idan an bayyana sakamakon zabe bayan karfe shida na yamma, sai su ce wa ogogin ma su ai cincirindon matasa ne suka mamaye wurin, har suka fi karfin su.

Share.

game da Author