ZABE: Za a yi amfani da jami’an tsaro na NSCDC 1,050 a jihar Zamfara

0

Rundunar tsaro na NSCDC a jihar Zamfara ta bayyana cewa za ta yi amfani da dakarun ta 1,050 wajen kula da zabe da za a yi a jihar Zamfara.

Shugaban hukumar Garba Aliyu ya fadi haka da yake zantawa da manema labarai a garin Gusau ranar Talata.

Aliyu yace wadannan jami’an tsaro za su samar da tsaron ne a rumfunan zabe 2,516 dake kananan hukumomi 14 a jihar.

Ya kuma ce hukumar ta kebe wasu ma’aikatan da za su sa ido a aiyukkan zabe da zai ayi a wasu kananan hukumomin dake karkashin shiyoyi uku na jihar.

” Akwai kuma wasu ma’aikatan da za su zauna a shirin ko ta kwana da kuma samar da tsaro a hedikwatar jihar inda za a tattara kuri’u gaba daya.

A karshe Aliyu ya yi kira ga mutane musamman matasa su tabbata basu tada rikici a lokacin zaben ba yana mai cewa duk wanda aka samu yana neman tada zaune tsaye zai kuka da kan sa domin ashirye suke da su tabbatar da zaman lafiya a jihar a wannan lokacin.

Share.

game da Author