Dalilin soke muhawarar ‘yan takarar gwamnan jihar Kaduna – NIPR

0

Jami’in hukumar NIPR a jihar Kaduna Bashir Chedi ya bayyana cewa hukumar ta soke mahawarar ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna ne a dalilin rashin amincewar ‘yan takaran.

Chedi ya ce hukumar ta shirya wannan mahawara ne domin kara wayar da kan mutane game da zaben shugabanni na gari kafin lokacin zabe.

” Da muka nemi yan takarar su amince da wannan muhawara, wasu sun ba mu sharadin da ba za mu iya cikawa ba sannan wasu sun fito karara sun nuna rashin amincewar su da taron.

” Taron muhawarar ‘yan takara al’ada ce da ta dade a kasashen da suke amfani da tsarin mulki na dimokradiyya a duniya. Yin haka na samar wa mutane damar zaben shugabanni na gari sai dai ‘yan siyasan Kaduna sun ki amincewa da haka.

Chedi ya ce hukumar za ta bada karfi wajen ganin ‘yan siyasan jihar sun yarda da ayi irin wannan muhawara da nan gaba.

Ya kuma yi kira ga mutane kan kiyaye duk sharuddan da dokokin zabe domin ganin an yi sabe cikin kwanciyar hankali a jihar.

Share.

game da Author