Osinbajo ya karyata rade-radin yin Murabus daga kujerar mataimakin shugaban kasa

0

Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya karyata rade-radin da ake ta yadawa wai ya yi murabus daga kujerar mataimakin shugaban Kasa bisa dalilin wai kin gayyatar sa taron majalisar tsaro ta kasa da aka yi.

A yau Alhamis ne aka tashi cikin rudu musamman a shafunan yanar gizo inda aka rika yayadawa wai mataimakin shugaban kasa cikin fushi ya mika takardar yin murabus din sa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a bisa wai don an ki gayyatar sa taron kwamitin tsaro da aka yi a fadar gwamnati.

” Wannan kisisina ce da makirci daga abokanan adawar mu ganin cewa zaben shugaban kasa ya rage kwanaki biyu kacal a yi shine aka kulla wannan abu don a tada hankulan jama’a.

” Watsa irin wannan labari ma ba tare da an tantance ba bai dace ba sam-sam. A dalilin haka ina so in tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ina nan daram dam tare da shugaba Muhammadu Buhari. Kowa yayi watsi da wannan zance.

Share.

game da Author