Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa tsakanin ranar 4 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2019 mutane 37 ne suka kamu da Zazzabin Lassa a kasar nan.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya sanar da haka ranar Laraba inda ya kara da cewa adadin yawan mutanen dake dauke da cutar yanzu ya kai mutane 324 sannan wadanda suka rasu kuwa yanzu sun kai 69.
Ihekweazu ya jero jihohin da ake fama da wannan cuta kamar haka: Edo, Ondo, Bauchi, Nasarawa, Ebonyi, Plateau, Taraba, FCT, Adamawa, Gombe, Kaduna, Kwara, Benue, Rivers, Kogi, Enugu, Imo, Delta, Oyo da Kebbi.
Ya kuma ce wasu ma’aikatan kiwon lafiya uku sun kamu da cutar daga jihohin Benue, Bauchi da Ribas.
” A yanzu haka adadin yawan ma’aikatan kiwon lafiya da suka kamu da cutar a kasar nan sun kai 12 daga jihohin Edo, Ondo, Ebonyi, Rivers, Bauchi da Benue sannan daya ya mutu a jihar Enugu.
Ihekweazu ya ce cibiyoyin kula da masu dauke da cutar sun duba mutane 3,746 da ake zargin sun yi mu’amula da mutanen da suka kamu da cutar daga jihohi 18 inda daga ciki aka sallami 1,045.
Ya ce cibiyoyin kula da wadanda suka kamu da cutar za su kara sa himma wajen ganin an dakile yaduwar cutar a kasar nan.
Hanyoyin guje wa kamuwa da zazzabin lasa sun hada da:
1. Da zaran mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.
2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.
3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci neasa da fitsari da kuma kashin beraye.
5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi.