Jin irin kalaman da dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo ya rika yi bayan kungiyar su ta Juventus ta sha kashi a hannun Atletico Madrid a daren Laraba, zai sa mai karatu ya tabbatar da cewa daga Ronaldo har Juventus ba wanda ya ji dadin kwallaye 2:0 da aka kwarara wa Juventus din.
Ronaldo ya shiga birnin Madrid da kwarin guiwa, kasancewa shi ne birnin da ya shafe shekaru tara ya na wasa a kungiyar Real Madrid, kuma ya saba kafsawa da Atletico sau da dama.
“To sai me, ni fa sau biyar na taba cin Kofin Champions League, ku kuma ko sau daya ba ku taba daukar kofin ba.” Haka Ronaldo ya goranta wa Atletico da magoya bayan ta a lokacin da suke ficewa daga cikin fili bayan tashi daga wasan.
Masu sharhin wasanni sun ce a shekaru takwas da Diego Simeone ya yi ya na horas da ‘yan wasan Atletico, ba su taba yin wasan bakin rai bakin fama ba, na nuna gajinta, kamar yadda suka yi a jiya Laraba, bayan komawa daga hutun rabin lokaci ba.
Wannan bajinta da suka nuna kuwa ta na nufin cewa yanzu kungiyar ta karkata ne kai-tsaye wajen tabbatar da cewa ta ci Kofin Zakarun Turai, wanda shi kadai ne ba ta taba samun nasarar dauka ba.
Tun da farko dama ba a yi wa Ronaldo kyakkayawar tarba a cikin filin kwallon ba. A lokacin da suke atisaye, kafin a fara wasa, an rika yi masa eho da sowa. Sannan kuma da aka fara wasa, duk lokacin da ya taba kwallo sai ‘yan kallon su rika hura masa usur da karfi.
Kafin a tafi hutun rabin lokaci sai da dan wasan Juventus, Mattia De Sciglio ya kayar da dan gaban Atletico, Diego Costa. Alkalin wasa ya hura bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma daga baya na’urar tantancewa ta nuna a wajen yadi 18 aka yi kayen, ba a ciki ba.
‘YAN KALLO SUN HARZUKA RONALDO
An kusa tashi daga farkon rabin lokaci ne Ronaldo ya yi tsalle ya yi wata irin faduwa, a lokacin da dan bayan Atletico Juanfran ya kai masa harbi da kafar sa a kan kauri.
Maimakon magoya bayan Atletico su tausaya masa, sai suka rika antaya masa ruwan ashariya, wadanda ba su rubutuwa a jarida. Wannan ta sa Ronaldo ya rika daga musu yatsu biyar, wato nufin sa, shi dai ya taba daukar Kofin Champions League sau biyar, su kuma ko sau daya ba su taba dauka ba. Biyu daga cikin su kuwa ya dauke su ne bayan kafsa wasan karshe tsakanin Real Madrid da ita Atletico Madrid din.
Morata da Juventus ta sallama zuwa Chelsea, daga baya cikin watan Janairu din nan ya koma Atletico, shi ne ya taimaka aka jefa wa Juvestus kwallon farko. Gimenez ne ya jefa kwallon.
Sai kwallo ta biyu kuma wadda Wojciech Szczesny ya jefa bayan ta gogi kugunn Ronaldo, ta fada raga.
Da alama Atletico ta rantse da ita za a yi wasan karshe, kuma ta dauki kofi a sabon filin ta na Wanda Metropolitano da ta bude ba da dadewa ba. A wannan fili ne za a buga wasan karshe a Kofin Zakarun Turai, wanda shi kadai ne Atletico ke bugawa.
Girona ta fitar da ita a Kofin Del Rey, sannan kuma cin da Madrid ta yi mata har gida 1:3, ya sa ta daina mafarkin daukar Kofin La Liga.
Idan aka yi duba da yadda tarihin kwallo ya ke a tsakanin kungiyoyin biyu, wato Atletico da Juventus, za a ga cewa a gasar Champions League a zagayen siri-daya-kwale, ba a taba cin Juventus kwallaye 2 har ta rama su a wasa na gaba ta yi nasara ba.
Ita kuma Atletico sau 25 idan ta yi nsara a was an farko, ba a rama kwallayen har a yi nasara a kan ta.
RONALDO: KWALLIYA BA TA BIYA KUDIN SABULU BA
Ko shakka babu kungiyar Atletico ta guma wa Ronaldo da Juventus tsiya. Dan wasan da suka fara asusun banki suka saya da tsadar gaske, da sa ran zai taimaka musu su dauki Kofin Zakarun Turai a wannan shekarar, bai tabuka musu abin a zo ga gani a gasar ba.
A wasanni shida da Ronaldo ya buga na Gasar Champions League, kwallo daya tal ya ci. Sannan kuma a jiya shi ne ya yi sanadin jefa musu kwallo ta biyu a cikin raga. Domin a kokarin da ya yi ne wajen tare Godin kaiwa ga kwallo, ta bugi kugun Ronaldo din, ta afka cikin ragar su.
Ko ya za su karke a wasa na biyu a birnin Turin?