Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ya yi bayanin cewa ta kammala gagarimin aikin sake saisaita na’urar tantance katin rajista.
Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a raron sa na uku da manema labarai, tun bayan dage zabe da aka yi cikin makon da ya gaba.
An dai dage zaben ne daga ranar 16 Ga Fabrairu da 2 Ga Maris, zuwa 23 Ga Fabrairu da kuma 9 Ga Maris.
A taron na sa da manema labarai, ya ce an samu nasara saisaita na’urorin baki daya.
“Ina mai farin cikin shaida muku cewa an cimma nasarar sake saisaita na’urorin tantance katin masu jefa kuri a baki dayan su.” Haka Yakubu ya bayyana a jiya Laraba.
Kowace na’ura an saita ta ne da runfar zaben da za ta yi aiki da ita, kuma ba zai yiwu a iya bude ta har a yi aiki da ita ba sai zuwa ranar Asabar daga karfe 8 na rana.
Ya ce an yi haka ne saboda guje wa magudi kafin zabe.
Shugaban na INEC ya ce duk an kashe na’urorin tun karfe 10 na dare, ba za a iya bude su ba har sai ranar Asabar karfe 8 na safe, lokacin da za a fara zabe.
Dama dai INEC ta gayyaci dimbin jami’an Babban Bankin Najeriya, CBN da su tabbatar da sahihancin na’urorin wadanda aka maida cikin satin da ya gabata, bayan INEC din ta dage zabe.
Discussion about this post