Dalilin daya sa muka kama darektan yada labaran jam’iyyar PDP na Kaduna – SSS

0

A yau Talatan ne hukumar tsaro na SSS ta bayyana dalilin da ya sa ta kama darekta yada labaran jam’iyyar PDP Ben Bako Ranar Asabar a garin Kaduna.

Jami’in hukumar AI Koya ya sanar da haka inda ya kara da cewa kama Ben Bako da suka yi ranar Asabar a garin Kaduna ya zama dole saboda samar da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya a dalilin kalamai da ya fadi da ka iya tada zaune tsaye a jihar a wajen Kamfen din Jam’iyyar PDP a garin Kafanchan.

Idan ba a manta ba a jiya Litini ne Jam’iyyar PDP ta yi kira ga jami’an tsaro na SSS da ta gaggauta sakin Darektan yada labaran jam’iyyar Ben Bako da ta waske da shi ranar Asabar da yamma a garin Kaduna.

Jigo a jam’iyyar Danjuma Sarki ya sanar da haka ranar Lahadi da yake zantawa da manema Labarai a garin Kaduna inda ya kara da cewa jam’iyyar ba za ata taba yin abinda zai zubar mata da kima a idanun mutanen jihar ba ko kuma a lokacin zabe.

Sarki ya Kara da cewa Jam’iyyar PDP ba Jam’iyyar tada husuma ba ce. Sannan ba zata yi abinda zai sa a yi tashin hankali a lokacin zabe ba.

Share.

game da Author