Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa akalla na’urar tattance masu jefa kuri’a 4,695 ne suka kone kurmus a ofishin ta da ke jihar Anambra.
Wutar wadda ta tashi jiya Talata, ta faru ne kwana biyu bayan tashin wuta a ofishin INEC da ke karamar hukumar Qua’an Pam ta jihar Filato, mako guda kuma bayan tashin wata wutar a wani ofishin na INEC a daya daga cikin kananan hukumomin jihar Abia.
Daraktan Yada Labarai da wayar da kai na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
PREMIUM TIMES ta rigaya ta buga labarin na yadda kwantina biyu dauke da na’urar tantance masu jefa kuri’a ta ci wuta a hedikwatar INEC da ke Awka.
Wannan ce gobara ta uku a cikin kwanaki 12 a ofisoshin INEC daban-daban a fadin kasar nan.
INEC ta ce wannan koma-baya ne wajen gudanar da zabe a jihar Anambra. Sai dai kuma ta ce za ta gaggauta kalato wasu na’urorin tantance masu zaben daga wasu jihohi domin a cike gurabun wadanda suka kone a jihar Anambra.
INEC ta ce ta na da yakinin cewa za a gudanar da zabe a jihar Anambra a rana daya da sauran jihohin kasar nan.
Hukumar ta kuma sanar wa jami’an ‘yan sanda gobarar, inda ta kara da cewa ta jiran sakamakon rahoton ‘yan sanda.