Ba mu rigima a kan kudaden kamfen -PDP

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa babu wata rigima ko rashin jituwar da ta taso a kan kudaden kamfen a cikin jam’iyyar, a baya ko a yanzu.

Kakakin PDP Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka a Abuja a jiya Litinin.

Ya ce wannan zargi da wasu ke yadawa abin dariya ne, kuma yarinta ce da rashin tunani.

Kola ya ce su na sane da irin farin jinin da dan takarar su Atiku Abubakar ke kara samu a kullum. Dalili kenan kan jam’iyyar ke hade, su na jiran nasara kawai bayan kammala zabe.

Ya ce jam’iyyar APC ce ke yawo ta na fesa gubar karya a cikin jama’a domin haushin da ta ke ji karsashin PDP dai kara habbaka ya ke.

Share.

game da Author