Yadda West Ham ta maida wa Liverpool hannun agogo baya

0

Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool ta zubar da damar ta na yi Manchester City tazarar maki biyar, bayan ta yi kunnen doki 1-1 da kungiyar West Ham United, a babban filin wasa na birnin Landon.

Dan wasa Sade Mane ya jefa kwallo a ragar West Ham tun kafin hutun rabin lokaci.

Sai dai kuma murna ta koma ciki ga magoya bayan Liverpool bayan da Michael Antonio ya jefa kwallo a ragar su, kuma aka tashi wasan a 1-1.

A yanzu maki uku ne kadai tsakanin Liverpool da Manchester City. Amma kuma City za ta iya hawa zuwa ta daya idan ta yi nasara kan Everton a gobe Laraba.

Liverpool ta hadu da mishkiloli tun shigowar 2019, inda har yau sau biyu kacal ta yi nasara a cikin wasanni shida da ta buga a 2019.

Idan ba ta yi nasara a kan Bournemouth a ranar Asabar ba, to zanin ta zai kara kwancewa a kasuwa kenan.

Share.

game da Author