Maitaimaka wa gwamnan jihar Taraba Dairus Ishaku kan harkokin yada labarai Bala Dan-Abu ya bayyana cewa an sako sakataren yada labaran gwamnan Hassan Mijinyawa da masu garkuwa da mutanen suka yi a hanyar sa ta zuwa Gembu.
Dan-Abu ya sanar da haka ne wa manema labarai a garin Jalingo ranar Lahadi inda ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun sako Mijinyawa ne a daren Lahadi sannan yana ciki. Koshin lafiya.
Ya ce b ba biya kudin fansa ba a kansa.
Idan ba a manta ba a ranar 30 ga watan Janairu ne masu garkuwa da mutane suka sace Mijinyawa a hanyar sa ta zuwa Kamfen Gembu, Karamar Hukumar Sardauna.
Uwargidan Mijinyawa, Sekina Mijinyawa ta tabbatar da sace mijin nata da aka yi inda ta kara da cewa mijinta ya bar gida da karfe bakwai na safiyar Laraba zuwa tsaunin Mambila wajen Kamfen din gwamna Dairus.
A wanna lokaci Sekin ta roki masu garkuwan da su tausaya mata su saki mijinta da suka tafi da shi.
Yusuf Garba daya daga cikin mutanen da suka tsallake rijiya da baya daga tarkon masu garkuwan a wannan rana ya bayyana cewa masu garkuwan sun kama mutane da dama wanda a ciki har da wani bature dake kula da wani sansanin ‘yan gudun hijira.
” Bayan sun kammala kwace ababen dake hannun mutanen da suka kama sai suka kada su suka yi daji da su.”
Discussion about this post