Ana shirya yin murdiyya a zaben Abuja saboda Atiku ya kada Buhari – Inji gamayyar Jam’iyyu na CUPP

0

Gamayyar jam’iyyu na CUPP ta yi kira ga shugaban hukumar zabe da ya saka ido sosai kan zaben Babban Birnin Tarayya, Abuja, cewa ana ta kulle-kullen ganin an soke zabukan wuraren da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu nasara a zaben da aka yi jiya.

Kungiyar ta ce tunda aka ga ko kason 25 bisa 100 da ake bukata mutum ya samu ma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC ba zai samu aka shiga sakale-sakale tsakanin jami’an tsaro, wasu daga cikin ma’aikatan hukumar da ‘yan jam’iyyar APC domin a sanar cewa ba a kammala zaben Abujan ba sai an sake yin shi.

” Duk inda ake zabe an yi kuma sakamakon zabe ya nuna karara cewa Buhari cewa anyi wa Buhari mummunar kayi ne a zaben. Hakan yasa cikin su ya duri ruwa. Yanzu ana kokarin a tursasa wa shugaban Hukumar Zabe ne ya bayyana cewa zaben bai kammalu ba. Buhari fa ko kashi 25 bisa 100 da ake nema ma ba zai samu ba.

A dalilin haka ne kungiyar ta ke kira ga hukumar zabe, musamman shugaban ta Mahmood Yakubu da ya tsaya tsayin daka wajen ganin ba a yi nasara ba akan wannan shiri da suke yi.

Share.

game da Author