Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya sha kaye a karamar hukuma ta biyu cikin kananan hukumomi hudu da ya ke wakilta daga jihar Kwara.
Saraki mai takara a karkashin PDP, ya rasa kananan hukumomin ne ga dan takarar APC, Ibrahim Oloriegbe.
Bayan Karamar Hukumar Asa da ya rasa, ya rasa karamar hukumar Ilori ta Gabas.
Sanarwar da INEC ta bayar a yau Lahadi da rana, ta ce Saraki ya tashi da kuri’u 11,252 a karamar hukumar Asa, yayin da dan takarar APC kuma ya lashe kuri’u 15,923. Sannan kuma ya samu kuri’u 14, 654 a inda Ibrahim ya kwashi kuri’u 30, 014.
Sauran kananan hukumomi biyu suka rage.
Discussion about this post