Sakamakon zaben shugaban kasa daga jihar Adamawa ya nuna cewa jam’iyyar APC nasarar lashe kuri’un akwatin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da kyar.
APC ta samu kuri’u 216 a mazabar ta Gwadabawa, Yola ta Tsakiya, yayin da PDP ta samu 96.
Siyasar Adamawa na da jan hankali, kasancewa daga jihar ce dan takara PDP, Atiku Abubakar ya fito, haka uwargidan Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.
Ana kan tattara sakamako har yanzu na sauran wurare.
Discussion about this post