An gano maganin bada tazarar Iyali da maza za su iya amfani da shi

0

Likitoci a kasar Amurka sun gano wani magani mai suna ‘dimethandrolone undecanoate’ ko kuma DMAU da maza za su iya amfani da shi domin bada tazarar iyali.

Likitocin sun gano wannan magani ne domin samar wa maza damar taka mahimmiyar rawa a amfani da dabarun bada tazarar iyali.

Maganin DMAU na hana jikin namiji hada maniyi na tsawon wata daya inda koda ya sadu da mace a tsakain wannan lokacin mace ba za ta dauki ciki ba.

Hakan na nufin cewa jikin namiji zai ci gaba da hada maniyi kamar yadda ya saba yi idan ya daina amfani da maganin.

Wata jami’ar kiwon lafiya a Chicago kasar Amurka Monica Laronda ta ce gano wannan magani nuni ne na irin ci gaban da ake samu a fannin kimiya da sannan hakan zai taimaka wajen ba maza daman taka muhimmiyar rawa a harkar bada tazarar Iyali.

Sai dai har yanzu ba a kammala tattance ingancin maganin ba.

A Kwanakin baya cibiyar ‘Development Research and Project Centre (dRPC)’ ta shirya taro domin tattauna hanyoyin bunkasa amfani da dabarun bada tazarar iyali a Najeriya.

A taron ma’aikatar kiwon lafiya, masu fada a ji a fannin kiwon lafiya da wakilan gwamnati sun koka kan yadda mata kashi 11 bisa 100 ne a kasar nan ke amfani da dabarun.

Taron ya yi kira ga mutane da su dage da yin amfanin da dabarun bada tazaran iyali ganin cewa hakan zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar mace da na jariri.

” Ya zama dole fannin kiwon lafiya da masu fada a ji a fannin su zage damtse wajen ganin ana wayar da kan mutane game da mahimmancin amfani da dabarun bada tazarar iyali.

Share.

game da Author