Jami’an tsaro sun waske da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na Kaduna

0

Awowi 24 bayan waskewa da darektan yada Labaran Jam’iyyar PDP Ben Bako da jami’an tsaro na sirri suka yi, a yau Litini jami’an sun kame tsohon shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna, Yaro Makama.

Har yanzu ba a ba da dalilin kama wadannan jiga-jigan Jam’iyya ba.

Kakakin Kamfen din Jam’iyyar na Jihar Kaduna, Yakubu Lere ya bayyana cewa da farko jami’an tsaron sun gayyaci Yaro Makama ne ofishin su bayannan sai suka dawo bayan sun sallameshi suka tafi dashi Abuja.

Idan ba a manta ba jami’an SSS sun waske da Ben Bako ne bayan wani Bidiyo da ke nuna shi yana caccakar Jam’iyyar APC inda ya ke Kira ga mutane da su lakadawa duk Wanda ya zabi Jam’iyyar da ba PDP ba dukan tsiya.

Sannan Kuma yayi Kira da su tabbata sun kasa, sun tsare sannan sun raka kuri’u su bayan sun yi zabe.

Bayan bayyanar wannan Bidiyo ne jami’an SSS suka tarkata shi zuwa Abuja.

Shima Yaro Makama a na zargin cewa wasu kalamai ne da yayi a wajen Kamfen a Karamar Hukumar Lere ne yasa aka tarkata shi.

Da yawa daga cikin mutanen Jihar Kaduna suna kokawa bisa wannan kame da ake yi wa ‘yan Jam’iyyar Adawa cewa bai kamata a yi haka a wannan lokaci da zabe ya gabato ba.

Share.

game da Author