RANAR KORORO ROBA: Kungiya za ta raba kororo roba 600,000 a jihohi biyar a Najeriya

0

Kungiya mai zaman kanta ‘AIDS HealthCare Foundation (AHF)’ zata raba kororo roba 600,000 a jihohin Benuwai, Kogi, Nasarawa da Cross Rivers.

Jami’in kungiyar Steve Aboriade ya ce kungiyar za ta yi haka ne da yin Kira ga matasa da su tabbata suna amfani da kororo roba domin gujewa kamuwa da cututtukan da ake samu ta hanyar jima’I da kuma guje wa daukan cikin da ba a so.

” Amfani da kororo roba hanya ce na samun kariya daga kamuwa da cututtuka da ya Jada da sanyi, kanjamau da daukan cikin da ba a shirya wa ba.

A shekarar 2018 ne Hukumar NACA ta yi kira da kakkausar murya da ba masoya shawara da a kiyaye da saduwa da juna ba tare da kariya ba.

Shugaban hukumar NACA Sani Aliyu ya ce

” Ina kira ga masoya da su yi amfani da wannan rana na masoya don sanin matsayin su game da cutar Kanjamau. Kashi 17 bisa 100 ne kawai na matasa suka san matsayin su game da cutar Kanjamau, saboda haka ne ya zamo abin tsoro ga mutane da kowa ya shiga taitayin sa.

Ayi hattara, A raba soyayya ba Kanjamau ba.

Share.

game da Author