Wani dattijo mai shekaru 80, da dan sa ke Boko Haram, ya yi kira dan sa da ke Boko Haram da ya gaggauta yin saranda ga jami’an tsro kuma ya kama turbar zaman lafiya.
Dattijon mai suna Baba Modu, ya ce dan sa mai suna Ba-Ana ya shiga Boko Haram ne bayan an tirsasa shi, an hure masa kunne.
Da ya ke tattunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, dattijon ya ce ya yi matukar kokarin jan hankalin dan na sa da ya tuba ya mika kan sa ga jami’an tsaro, amma bai yi nasara ba.
Ya ce ya rabu da ganin dan na sa ne tun bayan kama shi da Boko Haram suka yi, aka tafi da shi cikin wata gona a dajin Karamar Hukumar Dikwa, aka ba shi horon Boko Haram, a cikin 2012.
Ya ce ya yi ta kokarin gano inda dan sa ya ke tun bayan kama shi da aka yi, har wata rana dai ya ji labarin ya na cikin ayarin kwamandojin Albarnawi, kuma aka fada masa inda zan iya samun sa.
“ Na ci tafiya har bakin Tafkin Chadi, domin na gano inda ya ke. Sai da na yi yawon sati daya kafin na gano inda ya ke.
“Lokacin da na je sananin da ya ke, na ce musu ni mahaifin Ba’Ana ne. Suka yi min tambayoyi da bincike, sannan suka ce ya tafi kai hari, na jira sai ya dawo.
“ Ba-Ana ya dawo cikin dare. Amma murya ta kawai ya ji, ya gane cewa ni ne mahaifin sa, kuma ya shaida musu.
“Na zauna a wurin su har kwanaki 30 ina kokarin karkato da shi, amma ya kekasa kasa ya ce ba zai daina Boko Haram ba.
Ya ce min ya na tsoron idan ya shiga hannun sojoji ba za su yafe mas aba, saboda ya kashe mutane da dama.
Amma duk da haka ban yanke kauna ba, ina rokon Allah ya sa wata rana ya daina, ya dawo gida.” Inji mahaifin sa.