SUNAYE: Sabbin jami’oin da gwamnatin tarayya ta amince da kafa su

0

A yau Laraba ne gwamnatin Tarayya ta amince da kirkiro sabbin jami’o’i masu zaman kan su ka kasar nan.

Ministan ilimi Adamu Adamu ya sanar da haka wa manema labarai bayan kammala zaman kwamitin zantarwa da ma’aikatar ta yi.

Jami’o’in da gwamnati ta amince da sune:

Jami’ar Greenfield a jihar Kaduna

Jami’ar Dominion a Ibadan jihar Oyo

Jami’ar Trinity a jihar Ogun

Jami’ar Westland a Iwo jihar Osun

A lissafe adadin jami’o’i masu zaman kan su a kasar ya kai 79 kenan.

Kafin amincewa da sabbin jami’oi hudu da aka yi yau, Najeriya na da jami’o’i mallakar gwamnatin tarayya 40 ne, Jami’o’i mallakar gwamnatocin jihohi 45 da masu zaman kansu 75.

An fara kafa jami’o’i masu zaman kan su a kasar nan ne a 1999 in da aka kirkiro da jami’o’i 3 da suka hada da jam’o’in Babcock, Igbinedion da Madonna.

Share.

game da Author