Buhari ya yi magana a kan Akpabio da sauran wadanda suka koma APC don gudun bincike

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya maida raddi a kan zargin cewa jam’iyyar APC na bai wa wadanda suka wawuri kudade mafaka kuma su ke gudun bincike.

Buhari ya ce ba zai taba kyale duk wani da aka kama da laifi dumu-dumu kuma aka samu shaida kwakwara ba.

Ana ci gaba da zargin yadda EFCC ke bincike, inda ake ganin ta fi karkata ga wadanda ke cikin jam’iyyar adawa, ta na kyale wadanda suka yi tsallen-badake suka koma APC.

Buhari ya kafa dalili da Joshua Dariye da Jolly Nyame da ya koma APC kuma aka gurfanar da shi a ka daure.

Ko jiya Talata sai da mataimakin jam’iyyar PDP na Arewa, Babayo Gamawa ya fice daga PDP ya koma APC.

Ya koma ne alhalin an rigaya an gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya ta Bauchi, bisa laifin karbar naira milyan 500 daga tsohuwar ministar fetur, Diezani Allison-Madueke.

Fadar Shugaban Kasa ce da kan ta ta yi sanarwar komawar ta sa PDP.

A cikin hirar Buhari da THISDAY, ya ce masu cewa Godswil Akpabio ya koma APC ne domin ya tsere wa hukunci, sun yi masa rashin adalci.

Idan ba a manta ba, EFCC na neman naira bilyan 108.1 a hannun Akpabio. An kama shi sau biyu bayan hawa mulkin Buhari. Amma tun da ya koma APC cikin 2018, ba a sake tayar da zancen ba.
Bahari ya ce ya na kalubalantar mutane su nuna masa mutum daya da ya ce kada a bincika.

Share.

game da Author