Sakamakon binciken da wasu kungiyoyi masu zaman kan su suka yi ‘Occupational Knowledge (OK)’ da na (MSF) ya gano wasu hanyoyin da za a iya bi wajen kiyayewa daga fadawa hadarin shakar gurbataccen iskar da kan taso idan a na wannan aiki sannan kan yi sanadin rasa rayukan mutane musamman yara kanana.
Binciken ya nuna cewa in gurbataccen iskar da ake shaka na matukar yi wa mutum illa dake kawo illa ga huhu, ya kan sa akam da cutar zuciya ma.
OK da MSF sun gudanar da wannan binciken ne a dalilin mutuwar da yara sama da 400 suka yi a jihar Zamfara a 2010 saboda shakar irin wannan gurbataccen iska.
Bayan shekaru biyar sai ya sake aukuwa a jihar Neja a shekaran 2015 inda yara 30 suka rasu a dalilin haka.
Kungiyoyin sun bada shawarar a rika watsa ruwa a irin wadannan wurare domin ragewa da tashin kura da irin wanna gurbataccen iska da yakan kai ga a shaka.
Jami’in kungiyar likitocin jinkai Perry Gottesfeld, ya bayyana cewa wayar da kan ma’aikatan dake hako ma’adanai game da illolin shine mafita, da kuma amfanin amfani da ruwa a wajen da suka wannan aiki.