Na daina kallon Madrid idan ba ta sa Isco wasa ba – Van der Vaart

0

Tsohon dan wasan Madrid, Rafeal Van der Vaatt, ya nuna cewa dan wasan Madrid, Isco fitacce ne a duniya.

Ya nuna cewa ya na takaicin dalilin da ya sa kocin Madrid, Santiago Solari ba ya sa Isco wasa daga farko.

A fusace ya ce ba zai sake kallon wasan Madrid ba, muddin ba a saka Isco daga farko ba.

Rabon da Isco ya fara wasa tun cikin Octoba, sai an kusa tashi ake shigo da shi.

Wannan abu ya bata masa rai matuka, kuma ya haifar da sabani, har shi kan sa ba neman barin kulob din.

Rafeal ya ce ya na fatan wasan da Madrid za ta kafsa da Ajax, za a saka Isco daga farko. Amma idan Solari bai sa shi daga farko ba, Rafeal ya ce ficewa zai yi daga filin.

Ingila

Mai horas da ‘yan wasan Manchester City, Pep Gordiola, ya hori ‘yan wasan sa da su daina damun kan su da fatan Liverpool ta sha kashi a wasannin ta ba gaba.

Gordiola ya ce su dai su maida hankali wajen yin nasara kawai.

Man City ce ya biyu daga Liverpool da ratar maki hudu. Ya ce idan suka zauna su na duban wasannin da Liverpool za ta buga a gaba masu zafi, to su kuma hankalin su na zai koma a kan yadda za su yi nasarori a wasannin su na gaba ba.

Har ila yau daga kasar na Ingila, tsohon dan wasan Chelsea da a yanzu ya ke buga wa kungiyar Arsenal wasa a Ingila, Petr Cech, ya bayyana cewa zai yi ritaya a karashen kakar wasan wannan shekara ta 2019.

Jin haka ne Chelsea ta yi masa albishir cewa za ta ba shi aikin zama jakadan kungiyar ko kuma horas da karamin kulob din kungiyar.

Cech ya shafe shekaru 11 a Chelsea, kafin ya koma Arsenal.

Share.

game da Author