Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta cire sunayen ‘yan takarar majalisar tarayya da na majalisar dattawa na jihar Ribas da Zamfara.
Wannan ya kara tabbatar da cewa INEC ba ta za bari su yi zabe ba, kamar yadda dokar zabe ta kasa ta gindaya.
INEC ta fito da jerin sunayen ‘yan takarar shugabancin kasa, na ‘yan takarar sanata da na majalisar dattawa kuma ta buga a shafin ta na intanet.
Ta buga sunayen ne jiya Alhamis, kamar yadda doka ta gindaya, cewa a ranar 17 Ga Janairu za ta buga sunayen masu takarar shugabancin kasa da na majalisar dattawa da ta tarayya.
Su kuma na gwamnoni da na masu takarar majalisar jiha, sai a ranar 31 Ga Janairu ne za a fitar da su.
Sakatariyar INEC, Rose Orianran-Anthony ce ta sa hannu a jerin sunayen masu takarar da hukumar zaben ta fitar jiya Alhamis.
Jihar Ribas dai Babbar Kotun Tarayya ce ta haramta su shiga zabe, ita kuma Zamfara rikici ya sa ba a gudanar da zaben fidda-gwani ba, har wa’adin da dokar hukumar zabe ta gindaya ya fice.