Katsina za ta fara sabule wa ragwayen wakilan Majalisar Tarayya na jihar wando a kasuwa

0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya bayyana cewa daga wannan zabe mai zuwa, duk dan Majalisar Tarayya da aka zaba daga jihar Katsina ya je ya ki tabuka komai, to za a yi masa kiranye ya koma mazabar sa.

Masari wanda tsohon Kakakin Majalisar Tarayya ne, ya bayyana haka a lokacin kamfen a Karamar Hukumar Kaita, a jiya Talata.

Sai dai kuma duk da haka, ya ce ya na da yakinin cewa ‘yan majalisar jihar Katsina ba za su je Abuja su dumama benci ba.

Masari ya kuma roki al’ummar da suka taru da kuma gaba dayan jihar cewa a yi APC sak.

Share.

game da Author