Dan wasan Chelsea ta Ingila Eden Hazard da kungiyar Real Madrid ke ta zawarci, ya ne neman zame wa kungiyar nakiyar kan kashi, domin rahotanni sun ce an sargafa masa farashi har na Fam miliyan 100.
Idan mai karatu ya na so ya gane ko nawa Chelsea ke nema daga duk mai son sayen Hazard, to sai ya lissafa fam milyan 100 sau naira 430.
Sannan zai iya gane ko naira biliyan nawa ta ke nema.
Haka dai jaridar Telegaraph ta Ingila ta buga, cewa Chelsea ta ce saura watanni shida kwangilar Hazard ta kare a kungiyar.
Da wahala Madrid ta kwashi wannan kudi ta saye shi, duk da dai ita ce kungiyar da ta fi kowace a duniya wajen yin kumumuwar sayen dan wasa duk tsadar sa.