Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa tarihin Najeriya ba zai cika ba sai fa ana ambato daruruwan gudunmawar da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa kasa Najeriya.
Obasanjo ya kara da cewa shugaba Buhari yayi abin a yaba masa, sallamar sufeto janar Idris Ibrahim da yayi bayan ya kai lokacin yin murabus a aikin ‘dan sanda.
” Hakan da yayi ya kyauta matuka ganin cewa Sufeto Idris yayi kaurin suna wajen iya shirya magudin zabe.
Babban addu’ar da nake yi shine Allah yayi wa Buhari tsawon kwana, ya ga yadda Najeriyar da ya gina abin da ta zama.
Obasanjo ya yi kuma amfani da wannan dama domin yin kira ga shugabannin kasashen Afrika da su maida hankali wajen ganin an dakile matsalar ayyukan ta’addanci da ke neman ya addabi kasashen.
Ya ce a yanzu da ake ganin an gama da kungiyoyi irin na ISIS a kasashen larabawa, yanzu duk zasu karkato ta yankin Afrika ne saboda haka yake kira ga shugabannin kasashen da su maida hankali a kai matuka.
Daga nan sai Obasanjo ya roki shugaba Buhari da ya tabbata an yi zabe mai nagarta a kasarnan, zaben da duk duniya za su yaba sannan kuma ya yi kira ga shugaban Hukumar Zabe Yakubu Mahmood, da ya ba marada kunya.