Fadar Shugaban Kasa ta bayyana tsohon shugaban kasa, Osulegun Obasanjo da cewa ya na bukatar likita ya duba lafiyar sa, sannan kuma ta yi masa fatan Allah yaba shi sauki cikin gaggawa.
Hakan ya biyo bayan doguwar wasikar da Obasanjon ya raba wa manema labarai a jiya Lahadi, inda ya yi wa gwamnatin Buhari da shi kan sa Buhari din kakkausar suka.
Obasanjo ya nuna cewa ganganci ne da kuma saida rai idan har ‘yan Najeriya suka sake zaben Buhari.
Ya kuma yi zargin cewa INEC a karkashin Buhari ba za ta yi adalci ba, inda ya kafa hujjoji, ciki har da zaben da ya gudana a jihar Osun.
Obasanjo ya ci gaba da cewa Boko Haram ya yi karfi a yanzu fiye da a can baya.
Sai dai kuma a cikin martanin da Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ya maida wa Obasanjo, ya ce dattijon ya ga ba shi da wata madogara ta siyasa da zai iya ja da Buhari, shi ya sa ya koma ya na kitsa tuggu da kisisina.
Ya kara da cewa tun daga lokacin da Obasanjo ya bar mulki cikin 1979, har yau bai kyale kowace gwamnati da aka yi bayan sa ba. Sai ya rika yin kokarin da ya yi ya na yi wa kowane shugaban kasa katsalandan.
Ya ce hatta shugaban da shi Obasanjo din ya dauko don son ran sa, ta hanyar karya ka’idodin jam’iyya, ya zama shugaban kasa, shi ma bai bar shi ba.
Ya kara da cewa dama haka Obasanjo ya ke, idan ya ga ya kasa sarrafa akalar wani shugaba yadda ya ke so, to sai ya rika shirya masa tuggun da ya saba har ya zama uban ‘yan harkalla ko ma kakan ‘yan harkallar dukiya kamar yadda Majalisar Dattawa ta bayyana yadda ya ke.
Garba ya jaddada cewa kamar yadda shugaba Buhari ya sha fada, zaben 2019 zai kasance mai adalci kuma sahihi.
“Abin da Obasanjo da sauran yaran sa da ya ke wa kore, ‘yan PDP ya kamata su sani, shi ne za mu koya musu hankali a wannan zaben mai zuwa.
Za su gane kuren su, domin rata da tazatar da za a ba su a wannan karo sai ta fi ta zaben 2015.
Ya kuma karyata zargin da Obasanjo ya yi cewa APC ta fara tsara yadda za ta ci zaben 2019, ta hanyar nada jami’an tattara kuri’u na boge, wadanda tuni ya ce sunn fata tantance yawan kuri’un da za su bai wa kowane dan takara.
Obansanjo ya ce kuri’a ko yawan magoya baya ba za su yi tasiri ba a zaben 2019. Wannan ne fadar shugaban kasa ta ce karya ya ke yi tsofai-tsofai da shi.
Garba ya tuna yadda Obasanjo ya almubazzarantar da dala bilyan 16 wajen gyaran wutar lantarki, amma kwan lantarki bai samar wa ‘yan Najeriya ba.